Saduwa Da Namiji Ga Mace Mai Ciki Na Kawo Saukin Haihuwa – Likita

Saduwa Da Namiji Ga Mace Mai Ciki Na Kawo Saukin Haihuwa – Likita

0 304

Wani kwararren likitan mata dake asibitin kasa dake Abuja Chris Agboghoroma ya bayyana cewa yawan saduwa da namiji ga mace mai ciki musamman lokacin da ta kusa haihuwa na taimakawa wajen hanzarta kawo nakuda da saukin haihuwa.

Karanta: Wasu Abubuwa 10 Dake Sa Maza Gudun Mata Bayan Sunyi Jima’i da Su

” A lissafe kamata ya yi mace mai ciki ta haihu cikin makonni 38 ko 42 amma saboda wasu matsaloli ta kan wuce wannan lokaci.

Ya Kara da cewa mace mai ciki za ta iya guje wa irin haka idan tana saduwa da mijin ta akai-akai idan ta kusa haihuwa.

Bayan haka ya karyata wannan camfe-camfen da ake yadawa wai babu kyau mace ta sadu da mijin ta Idan tana da ciki, musamman Idan ta kusa haihuwa.

” Bari ku ji ma , rashin haka matsala yakan jawo wa mace Idan ta zo haihuwa.

Karanta: Jana’izar Sojoji 1,000 A Asirce Ya Zama Wajibi Gwamnati Ta Bincika – Atiku

Kafin ya kammala bayanan sa, likitan ya yi Kira ga ma’aurata da su maida hankali wajen sanin matsayin mahaifar matan su yana mai cewa macen da ke da budadiyyar mahaifa yawan saduwa da ita Kan sa tayi barin cikin, amma Idan ba haka ba saduwa lokacin mace na da ciki lafiya ce.

To Magidanta Sai A Kara Himma Wajen Raya Sunnar Manzonmu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline