Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya: Ma’ana, Fa’idoji Da Rabe-Rabensu

1 11,960
Bugu
Bugu

Ma’anar Sana’a

Malam Bello A Muhammad ya bayyana cewa Hausawa na ganin sana’a a matsayin “Wata hanya ta sarrafa albarkatun kasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa dan Adam kamar amfanin gona, dabbobi, tsirrai, albarkatun da ke a karkashin kasa, Ya-Allah dutse ko cikin ruwa domin samun abin masarufi”.

 

Shi kuwa marigayi Malam Muhammad Balarabe Umar ya bayyana sana’a da cewa “Wata Hanya ce da dan Adam ya ta’allaka akanta domin samun abin masarufi”

Kira
Kira

Wadannan ma’anoni guda biyu sun fito da ma’anar sana’a a fili a matsayinta na duk wata sahihiyar hanya da mutum ke bin don samun abun dogaro da kai wajen gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum

 

A saboda haka ne ma za mu iya bayyana sana’o’in Hausawa na gargajiya a matsayin hanyoyin da Bahaushe ke bin tun tale-tale don samarwa kansa abin dogaro da kai.

Noma
Noma

Fa’idojin Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya

 

Duk wani abinda dan Adam ya ke yi yana da fa’ida ko akasin haka. Wani za ka samu fa’idarsa ta fi rashin fa’idarsa yawa, inda wani kuma rashin fa’idar shi ke da rinjaye. Amma duk wata sahihiyar sana’a ta Malam bahaushe da al’ummata ta yarda ta aminta da ita tana da fa’idoji kamar haka:

  • Bunkasa Tattalin Arziki Tsakanin Al’umma
  • Samar Da Abin Masarufi
  • Samar Da Aikin Yi
  • Haifar Da Wasu Sana’o’in
  • Raya Al’adun Gargajiya
  • Samar Da Magunguna Na Musamman
  • Inganta Dangataka Ta Hanyar Cudanya Da Jama’a

Ire-Iren Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya

Sana’o’in Hausawa na gargajiya sun kasu gida uku kamar haka:

  • Sana’o’in Maza
  • Sana’o’in Mata
  • Sana’o’in Tarayya (Maza Da Mata)

Wasu daga cikin sana’o’in gargajiya sun hada da: Kira, Farauta, Su, Jima, Gini, Rini, Fatauci, Sassaka da sauransu

 

Wasu daga sana’o’in mata sun hada da: Kitso, Kadi, Sana’ar kosai, Sana’ar kuli da mai, Daddawa, alkaki da nakiya, Sissika, Sirfe, Casa da dai sauransu

Sana'ar tuyar kosai
Sana’ar tuyar kosai

Daga cikin sana’0’in Hausawa na gargajiya da maza da mata suka yi tarayya akai kuwa akwai: Noma, Kasuwanci, Roko, Kiwo, Dillanci, Maganin gargajiya, Fawa, Ginin tukwane da sauransu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.