Dariya Zallah: Bafulatani Da Bahaushe A Birnin Abuja

Dariya Zallah: Bafulatani Da Bahaushe A Birnin Abuja

0 176

Wani bafilatani ne yaje babban birnin Nigeria Abuja, yana ta faman yawo a ciki Chan sai hango wani dogon gini mai hawa 20.

Abinka da mutumin daji ya saba da yan gidajensu kamar keji a daji sai yayi tsaye yana kallon wannan gidan saman mai hawa Ashirin yana ta mamaki yana dariya.

Karanta: Inyamurai Zasu Yi Da Nasanin Kin Zabi Buhari Ba – Inji Jam’iyyar APC

Chan sai yamma ta fara yi la’asar ta gabato sai ga wani bahaushe mai aikin gadi da unifom dinsa yazo ya iskeshi yana kallon benen.

Sai bahaushen nan ya daka masa tsawa! yace masa, kai kasan kallo daya naira hamsin ne, kallo nawa kayi?

Karanta: Dalilan Da Suka Sa ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Sai bafillace ya rude ya ce yallabai ayi min afuwa tuba nake kallo tara nayi, sai bahaushe yace dari hudu da hamsin kenan, kawo su ka ware kawai, karka bari akamaka, yace to,dan fulani ya zaro kudin ya miqawa bahaushe.

Sai da bahaushen ya wuce, yace sakarai baisan cewa ni ma daga gadi nake ba!

Karanta: Bullar Cuta: Mutum 213 Suka Kamu Da Zazzabin Lassa A Najeriya – WHO

haba sai Bafillace ya kwalla masa kira yace kai wawa kallo goma nayi baka ganiba yace: wawa kallo goma nayi baka ganiba

Sai Ya Arceeeee da gudu wai shi mai wayau!

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

You're currently offline