Jerin Abincin Da Bai Kamata Mutum Ya Ci Ba Kafin Ya Kwanta Barci

0 365

Masana lafiyar jiki sun bayyana cewa cin abinci a lokutan da basu dace ba yana kawo rashin natsuwa a barci.

Sun lissafa jerin abinci 5 da basu dace mutum ya ci ba kafin ya kwanta don samun barci mai dadi tare da nagarta.

1. Naman kaza: Naman kaza da sauran danginsa suna hana barci mai dadi matukar aka ci kafin barci. Wannan na faruwa ne saboda narkewar abinci a jikin dan adam na daukar lokaci yayin barci. A maimakon dan adam yayi barci mai dadi, jikinsa zai maida hankali ne wajen narkar da abincin.

2. Kayan kwalam masu sukari: Wannan a bayyane yake duk da mutane da yawa na cin irin wadannan abincin kafin su kwanta. Wannan ba abinda ya dace bane don kuwa suna daukar lokaci kafin su narke a jiki. A maimakon jikin mutum ya samu sauki da hutu yayin kwanciyar barcin, sai yayi ta kokarin narkar da abincin wanda hakan zai hana barci mai nagarta.

3. Shayin Coffee: Duk da kuwa abin sha ne, yana daya daga cikin abubuwan da yakamata a guda kafin a kwanta. Wannan kuwa za a iya danganta shi ne da sinadarin ‘caffeine’ da ke ciki wanda ke hana barci. Amma kuma idan mutum na da burin kin barci, toh zai iya shan coffee don wannan aikin. Abin kiyayewa a nan kawai shine kada ya zama mutum ya saba, don akwai matsalolin da ke akwai dangane da sabo da shan sinadarin caffeine.

4. Abinci mai yaji: Duk yadda mutum ke son abinci mai yaji, zai fi idan aka ci da safe ko da rana amma a kiyaye da dare. Abinci mai yaji kan jawo tashin zuciya idan aka ci da dare kuma hakan yakan hana nagartaccen barci.

5. Abinci mai maiko: A shawarce abinci mai maiko abin gudu ne da dare don samun lafiya mai inganci. Maikon da ke kunshe a abincin na sa ciki ya fitar da ‘acid’ wanda yake kawo tashin zuciya. A don haka ne idan ana bukatar barci mai nagarta tare da gudun tashin zuciya da safe, sai a guji abinci mai maiko da dare.

Karanta: Malaman Kwaleji 150 Sun Nemi Gwamnan Kuros Ribas Ya Biya Wasu Bukatunsu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline