Yadda Ake Girka Faten Doya Mai Alayyahu

0 40

Mujallar Alummata za ta koyar da yadda ake girka Faten doya mai Alayyahu wanda ba kowa ne ya san shi ba.

Kayan Hadi

• Doya
• Manja
• Alayyahu
• Nikakken ‘cray fish’
• Albasa
• Attarugu
• Tumatir
• Bandar kifi
• Nama
• Tafarnuwa
• Citta
• Magi
• Kori

Yadda Ake Hadawa

A sami danyar doya a fere ta a yayyanka ta kanana sannan a wanke a ajiye a gefe. Bayan haka sai a samu ganyen alayyahu shi ma a yayyanka amma manya-manya a wanke da ruwan gishiri sannan a ajiye a gefe. A silala nama da albasa da gishiri kadan sosai sannan a sauke.

A dora tukunya a wuta sai a zuba manja sannan a zuba yankakkiyar albasa da tafarnuwa da garin citta da yankakken attarugu da tumatir. A yi ta gaurayawa har sai sun soyu. Sannan a zuba ruwan nama da naman da magi da kori a wanke bandar kifi a zuba da ‘cray fish.’ Idan ya dan tafaso sai a dauko wannan yankakkiyar doyar a zuba a ciki. Idan ta dahu ta yi laushi sai a samu muciyar tuwo a dan farfasa doyar sama-sama yadda ruwan zai yi kauri sannan a dauko yankakken alayyahu a zuba na tsawon minti biyu zuwa uku. Idan ya nuna sai a gauraya a sauke.

Karanta: Yadda Shan Abarba Ke Kare Mutum Daga Kamuwa Da Cutar Daji – NIHORT

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline