Illolin Da Shan Ruwa A Tsaye Ke Haifarwa

0 41

Masana Lafiyar jiki sun bayyana cewa shan ruwa a tsaye yana da hatsari ga lafiyar jiki inda suka zayyano irin hatsarin da ke tattare da yin haka wanda sune:

1. Ciwon Gabobi: duk mai shan ruwa a tsaye na fuskantar barazanar kamuwa da ciwon gabobi musammam ma a lokacin tsufa. Wannan ya na faruwa ne a sakamakon ruwa da ya ke taruwa a gabobin fiye da yadda ya kamata.

2. Rashin Kashe kishi: bayan mutun ya sha ruwa a tsaye, nan da nan zai sake jin wani kishi.

3. Matsala ga koda ko mafitsara: koda ba ta iya tace ruwan da aka sha a tsaye yadda ya kamata. Wannan ya na sanya wa dauda da ke cikin ruwan ya makale a kodar, al’amarin da ka iya haifar da matsalolin mafitsara ko kuma ciwon koda.

4. Zai iya haifar da gyambon ciki (Ulcer) da kwarnafi (heart burn): A yayin da aka sha ruwa a tsaye, musamman ma idan kwankwada aka yi da sauri, ruwan zai bugi bututun da ke hade da baki da ciki da karfi, ya kuma bugi bangon cikin. Wannan ya na sa sinadarin acid da ke cikin ya dawo cikin bututun, al’amarin da idan ya ci gaba da faruwa, ka iya haifar da kwarnafi, da kuma gyambon ciki

5. Ya na hana abinci narkewa da wuri: Yayin da muke zaune ne jijiyoyin jikin mu ke iya samun nutsuwar narkar da abinci da wuri. Yayin da muke tsaye kuwa, yanayin da muke ciki ba irin wanda zai inganta haka ba ne.

Karanta: Yadda Ake Girka Faten Doya Mai Alayyahu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline