Yajin Da Aisha Buhari Ta Yi Nada Alaka Da Neman Auren Da Buhari Ke Yi

0 212

Rahoto daga Jaridar Point Blank News ta bayyana cece-kucen da jama’ar Nijeriya ke cigaba da yi na cewa uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi yaji daga fadar shugaban ƙasa, da zargin neman Minista Sadiya Faruq da ake wa Buhari.

Sadiya Faruq ‘yar asalin jihar Zamfara, bincike ya nuna cewa da akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin ta da mai girma shugaban ƙasa Buhari tun da daɗewa, rahotanni sun nuna cewar ta daɗe a tafiyar Buhari tun zamanin da ya yi takara a Shekarar 2011 lokacin Jam’iyyar CPC.

Karanta: Mutane 38 Sun Mutu A Hatsarin Kwalekwale A Kogin Kirfi A Bauchi

Tun a wancan lokaci jama’a suka fahimci da akwai soyayya da ƙaunar juna a tsakanin su da Buhari, amma zargi ne kawai saboda a wancan lokacin Sadiya Faruq tana da Miji, amma hasashen jama’a akan alaƙar Buhari da ita ya sake fitowa fili a wannan karon bayan mutuwar auren ta.

A zaɓen ministoci da Buhari ya yi ya zaɓo Sadiya daga Zamfara, kuma daɗin daɗawa shugaban ya ƙara bata shugabancin wata hukuma ta taimakawa ‘yan ƙasa da jarin kasuwanci wato (SPI) a taƙaice.

Amma a magana ta gaskiya dukkanin hasashen da jama’a ke yi na soyayya tsakanin Buhari da Minista Sadiya hasashen ne kawai, hakanan zargin da ake yi na cewar dalilin zargin neman da Buhari yake yi mata ne ya sanya uwargida Aisha Buhari barin fadar gwamnati na tsawon watanni, duka zargi ne wanda babu tabbas, domin tuni fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata cewa Aisha ta yi Yajin.

Sai dai kamar yadda aka sani shine, idan kaji gangami to da labari, kuma idan har babu Rami to mai ya kawo maganar Rami?

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline