Coci Ta Kori Malamin Da Ya Nemi Ya Yi Lalata Da Daliba A Jami’ar Legas

0 13

Cocin Foursquare Gospel Church a Nigeria ta bayyana sauke Dakta Boniface Igbeneghu, wanda yana daya daga cikin malaman jami’ar da aka nuna a bidiyon binciken BBC yana kalaman lalata ga ‘yar jarida, wadda ta yi badda-kama a matsayin daliba.

Dakta Boniface fasto ne a cocin, kuma cocin ta sanar a shafinta na Twitter cewa: “Shugabancin wannan coci ya samu labarin abin da aka nuna Dakta Boniface yana aikatawa a bidiyon binciken BBC Africa Eye.

“Cocin dai ta nesanta kanta daga abin da ya aikata sannan kuma ta yi alkawarin daukar matakin da ya dace.

“Kazalika ta bukaci faston da ya ajiye duk wani mukami da yake rike da shi a wannan coci mai albarka.”

Karanta: Lalata don bada maki: Ni ma da kyar na tsallake tarkon cin zarafin malaman jami’a – Mai dakin gwamnan jihar Ekiti

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da dabi’ar malaman da aka nuna a rahoton.

Ya rubuta cewa: “Yanzun nan na karanta labari game da #SexForGrades (lalata da malaman jami’o’i ke yi da mata domin ba su maki) a jami’o’in Yammacin Afirka. Ba za ta sabu ba, wajibi ne al’ummarmu ta dakile wannan dabi’ar.”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce dole ne a nemi hanyoyin hukunta malamai masu irin wannan halin.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline