Arzikin Ƙasar Nan Yana Hannun Jihohi Guda Huɗu – Shugaba Buhari

Arzikin Ƙasar Nan Yana Hannun Jihohi Guda Huɗu – Shugaba Buhari

0 85

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa akan yadda wasu tsiraru a kasar nan, suka danne tattalin arzikin ƙasar nan, in da yace akalla mutane miliyan 150 na cikin halin hannu baka hannu kwarya.

Karanta: ‘Yan Sanda Sun Kashe Shugaban ‘Yan Ta’addan Devil A Ribas

Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taro karo na 25 da ake gudana Abuja, mai taken wane hali Najeriya zata samu kanta a shekarar 2050.

“Najeriya kasa ce da ke da al’umma kusan miliyan 200 a cikin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja. Mafi yawan arzikin kasar ya na dankare ne a wasu jihohin da basu wuce guda huɗu ko biyar ba, tare da babban birnin tarayya. Wasu daga cikin attajiran kasar nan da su ke zaune a cikin wannan ɗakin su na da masaniya akan abin da na ke faɗa

“A haka ke nan jihohi 31 da ke da yawan mutane akalla miliyan 150 na zaman hannu baka hannu ƙwarya ne da ya sa a yanzu ƙasar nan ke fama da matsalolin tsaro da yaki ci yaki cinyewa.

Hakan yasa kasashen da ke kewaye da ƙasar nan na fama da irin wadannan matsaloli.

A ƙarshe Shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa zata maida hankali wajen ganin an tsara manufofin da zasu inganta tattalin arzikin kasar nan da kuma samar wa mutane sana’o’i da inganta zamantakewa a tsakanin mutanen ƙasar nan da tsaro.

Karanta: An Tsige Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba

Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki da kamfanoni masu zaman kan su domin bunkasa tattalin arzikin kasar nan da kuma tsara manufofi na ci gaban ƙasa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline