Shigar Malamai harkokin siyasa – Dakta Muhd Sani Umar Rijiyar Lemo

0 111

Mas’alar shigar Malamai cikin Siyasa mas’ala ce mai girma wacce ta wuce matsayin a mayar da ita abin wasan yara. A ce ta wayi gari a hanun kowa, har ya zama kowane dan ci da karfi yana da bakin magana da yin fatawa a cikinta.

A’a, mas’ala ce mai girma, wacce take bukatar Ijtihadin taron Malamai, babu Nassi ko Ijma’i a kanta, kuma ta zama “Mushkila” a cikin al’umma, ana matukar bukatar sanin hukuncinta, ana ganin Maslahar shigan Malamai harkokin Siyasa, amma a lokaci guda hakan yana tattare da matsaloli da kalu-bale masu yawa.

To yanke hukunci a kan irin wannar mas’alar ta fi karfi Malami guda daya, balle kuma a nakalto fatawar wani Malami da ya yi a kan wata kasa ayyananniya, ko wani hali ayyananne.

Mas’ala ce da ta kai matsayin manyan cibiyoyin Fatwa su zauna su kalle ta ta kowace fiska, su yi nazari a kan Kasar da ake wannar siyasar, su duba yanayin mazauna kasar da banbance-banbancen Addini da kabila da wayewa da suke da shi, su hangi barna da lalacewa da suka addabi kasar, da girman bukatar shigan Malamai cikin harkar ko rashinsa bukatar haka, da dacewar Malaman da kwarewarsu a harkar siyasa ko akasin haka, su kalli maslahohi da barna da ke cikin haka, su auna su rinjayar da abin da ya fi Maslaha ga Musulman wannar Kasa.

Wannan aiki ne na manyan cibiyoyin Fatwa, wadanda Malamai masu fatawa a cikinta sun siffantu da cikar ilimi da zurfin basira, da sauran siffofin Malamai masu Ijtihadi a kan manyan mas’alolin da suka damu Al’umma.

Akwai irin wadannan cibiyoyi na Fatawa, sawa’un a kasarmu Nigeria ne, kamar Kwamitin Fatawa da ke karkashin Majalisar Koli ta Addinin Muslunci, ko Ofishin Fatawa ta Kasar Misra, ko Majalisar Manyan Malamai a Jami’ar Azhar, ko Majalisar Manyan Malamai ta Kasa Mai Tsarki Saudiyya, ko Cibiyar Ilimin Fiqhu da take Jidda da sauransu.

Ita wannar mas’ala girmanta da muhimmancin ya kai a ce irin wadannan cibiyoyi na Fatwa da binciken Mas’alolin Addini ne ya kamata su ba da amsa su yanke hukunci a kanta.

A yi musu cikakken bayani a kan Nigeria, da yanayin al’ummar kasar, da yanayin siyasar kasar, da yanayin barna da lalacewar kasar da dukkan abin da yake da alaka da wannar mas’ala a kasar. Ku yi musu cikakken bayani a kan komai, sai su kuma su duba su auna komai bisa mahanga ta Shari’a, da yanayin Kasar, da ma’aunin Maslaha da barna, sai su yi Ijtihadi su yanke hukunci. Saboda Mas’ala ce da hukuncinta zai iya banbanta daga kasa zuwa wata kasa, da zamani zuwa wani zamani da hali da yanayi zuwa waninsa.

Wannan shi ya fi gamsarwa, a kan a mai da abin ya zama  abin wasa a hanun masu garaje, kowa ya zo yana yada dan guntun iliminsa, yana jifan mutane bata ko bidi’a ko munanan kalamai, yana hukunta mutane da abin da ba dalili ne na Shari’a ba.

Yaushe ra’ayin Malamin kungiyar ya taba zama hujja a kan mutane?

Abin takaici, jahilci ya sa an zo ana yanke hukunci a Addini da abin da ba hujja ne a Shari’a ba, har a danganta hakan da Salafiyya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline