Mahakan Gwal 52 Sun Rasa Rayukansu A Tafkin Chadi

0 34

Mutane 52 ne suka hallaka a arewacin Chadi sakamakon rubzawar wani ramin hakar zinare, yayinda suke tsaka da aiki, inda har yanzu jami’an ceto ke laluben wasu mahakan da dama da suka bace.

Da fari dai jami’an ceto a kasar ta Chadi sun ce mutane 30 suka hallaka, a lokacin da hadarin ya auku a yankin Kouri Bougoudi dake lardin Tibesti, a ranar talatar da ta gabata.

Kawo lokacin wallafa wannan labari dai, adadin wadanda suka jikkata ya tsaya a 37, kuma 21 daga cikinsu na cikin mummunan yanayi.

Karanta: Adam Zango Ya Maida Martani Ga Malamin Da Ya Zarge Shi Da Tara Mata Kanana Yana Fim Dasu

A baya bayan nan dai lardin Tibesti ya zama matattarar kungiyoyi masu dauke da makamai, da kuma gungun masu fasakauri dake sata ko hakar zinare ba bisa ka’ida ba.

A watan Janairu wani kazamin rikici tsakanin larabawan Libya mahakan zinare da kuma mahakan kabilar Ouaddai dake kasar ta Chadi, ya haddasa hasarar gwamman rayuka, lardin na Tibesti.

Chadi na daga cikin kasashen Sahel masu fama da matsalolin tsaro ta fuskoki da dama, da suka hada da barzanar mayakan Boko Haram, ‘Yan tawaye da kuma wasu kananan kungiyoyin sa kai masu dauke da makamai, sai kuma rikicin kabilanci da kuma tsakanin manoma da makiyaya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline