Mutane 55 Ne Suka Rasa Rayukansu a Sabon Rikicin Kaduna

0 20,011

A yau Juma’a ne gwamnatin jahar Kaduna ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a garin Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru a Kudancin jahar Kaduna a sakamakon barkewar rikici.

‘Yan sandan jahar sun ce an rasa rayukan kimanin mutane 55 a rikicin.

Toh sai dai akwai rade-radin cewa adadin wadanda suka rasu ya zarge haka.

‘Yan sandan sun ce sun kama kimanin mutane 22 da suke zargi na da hannu a lamarin.

A jiya Alhmmis ne rikicin ya barke a yayin da ake cin kasuwar garin. Jama’a da dama kan halarci wannan kasuwa daga sassa daban-daban na jahar da ma wasu jahohin.

Wani ganau ya shaidawa kafar yada labarai ta BBC cewa “muna tsaka da cin kasuwa kawai sai wasu matasa da suka yi kaurin suna wajen ta da irin wadannan fituntunu suka fado cikin jama’a da doke-doke suna karya rumfuna suna jidar kayan jama’a.”

Ya ce an kai har cikin dare ana tafka rikicin, sai da safe jami’an tsaro suka fara aikin tattaro gawarwaki.

Ya kara da cewa, an kona gidajen jama’a da rumfunan kasuwa da dama.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline