Adam A Zango Ya Koma Goyon Bayan Atiku

0 75

Shahararren jarumin Kannywood wanda aka sani da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen, Adam A Zango ya koma goyon bayan jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Ko a kwanan nan da ‘yan Kannywood din suka yi gangamin yakin neman zaben Buhari, Zango na kan gaba.

Sai gashi kwatsam ya sanya hoton shi tare da dan takara Atiku Abubakar ya rike hannunshi a shafinsa na Instagram.

Dama dai Zango ya taba fadin cewa ba a taba bashi ko sisi ba domin ya yi wa Buhari kamfen, inda ya nuna cewa kauna ce da soyayya kadai suka sanya shi yin haka.

Zango dai ya yi kira ga masoyansa da su dawo daga rakiyar APC su tattaru su yi wa Atiku kamfen.

Bangaren Kannywood da ke goyon Atiku tuni suka yi ta yi wa Zango marhaban da lale.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline