Abubuwa 5 Da Ke Haifar Da Yawan Tusa

0 171

Tusa na faruwa ne a sakamakon taruwar iska a ciki, wanda ko dai iskar shiga cikin ta yi daga waje ta baki, ko kuma ta samu ne a yayin narkewar nau’ikan abincin da muke ci.

Likitoci sun shaida cewa yin tusa sau 13 zuwa 21 a rana ba wani abu bane na tada hankali. Wannan abu ne da ka iya faruwa da kowa kuma ba ya na nufin ka na fama ne da wata cuta ba.

Idan tusa ta wuce wannan adadi ne a rana, toh za ta iya kasancewa ta cuta, kuma a nan ne ake bukatar mutum ya tuntubi likita.

Akwai dalilan da ke sanya wasu suna tusa fiye da wasu kamar haka:

  1. Yawan hadiya iska ta baki a yayin cin abinci
  2. Cin wasu nau’ikan abinci da ke fitar da iska da yawa yayin narkewarsu a ciki kamar su wake, madara, kwai da sauransu.
  3. Cin abinci da yawan gaske a lokaci guda
  4. Rashin narkewar abinci da wuri a ciki
  5. Rashin tauna abinci yadda ya kamata kafin a hadiye. Da sauransu.

Ga masu fama da wannan matsala, da fatan wannan dan takaitaccen bayani zai taimaka.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap Add to Home Screen
Add to Home Screen
AL'UMMATA Mujallar Hausa Lamba Daya
To install tap
and choose
Add to Home Screen
Continue in browser

You're currently offline